Friday, August 14, 2015

A yau dai a Nijeriya gwamnatin shugaba Muhammad Buhari ta kara fadada shirinta na yaki da cin hanci a dukkanin fadin kasar.
Mai girma shugaba Muhammad Buhari ya  nada wani kwamiti da ya kunshi tsofaffin shugabannin kasar da kuma shugabannin addinai da wasu manyan 'yan siyasar kasar. Shi dai wannan kwamiti shi ne zai dauki nauyin ganin an bi diddikin dukkan wata badakala ta cin hanci da rashawa da ta mamaye manyan hukumomin da ke tara ma kasar kudin shiga .