Saturday, August 1, 2015

Ma'anar waka.

Masana da drama sun bayyana ra'o'insu dangane da ma'anar wakar Hausa.Daga cikinsu akwai:
   Dangambo1982: "Waka wani furuci ne ko sako cikin azanci da ake aiwatarwa ta hanyar rerawa da daidaita kalmomi cikin wani tsari ko ka'ida da kuma yin amfani da dabaru ko salon armashi".
    Umar(1980) Yana cewa,"Waka tana zuwa ne a sigar gunduwoyin zantuka wadanda ake kira baitoci ko diyoyi kuma ake rerawa da wani irin sautin murya na musamman.
      Yahaya(1976:1) a gabatarwar da ya yi wa littafin Wakar Hada Kan Afrika cewa ya yi:" Waka magana ce ta fasaha a cure wuri daya a cikin tsari na musamman.
       Yahaya(1984) ya ce,"Waka maganar hikima ce da ake rerawa ba fada kurum ba wadda ke da wani sako da ke kunshe cikin wasu kalmomi zababbu,tsararru,kuma zaunannu".